in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Libya ta nemi tallafin MDD a bangarorin tattalin arziki da tsaro
2018-08-06 11:12:43 cri
Majalisar dokokin kasar Libya dake da mazauni a gabashin kasar, ta nemi tallafin MDD a bangarorin tattalin arziki da tsaro, sama da harkokin siyasa.

Mataimaki na farko na shugaban majalisar Fawzi Nuwairi ne ya yi kiran, yayin da yake ganawa a birnin Tripoli da Stephanie Williams, mataimakiya ta musamman ga Sakatare Janar na MDD kan harkokin siyasa.

Sanarwar da majalisar ta fitar, ta ce Fawzi Nuwairi, ya nemi MDD da ta dora muhimmanci kan bangarorin tattalin arziki da tsaro.

Ya kuma jaddada bukatar samar da cikakken tsarin da zai warware matsaloli siyasa da tsaro da tattalin arziki domin samar da zaman lafiya a kasar.

Matsalolin da suka hada da rashin tsaro da rarrabuwar kawuna a fannin siyasa da rashin tattalin arziki mai kwari ne ke kawo cikas Libya mai arzikin man fetur, tun bayan da rikicin 2011 da ya hambarar da tsohuwar gwamnatin Muammar Gaddafi.

Duk da yarjejeniyar da aka rattabawa hannu a watan Disamban 2015, wadda MDD ta dauki nauyi, har yanzu Libya na fuskantar rarrabuwar kawuna tsakanin hukumomi masu adawa da juna a yankunan gabashi da yammacin kasar, inda dukkaninsu ke kokarin neman hallaci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China