Bidiyon da aka fitar a ranar Juma'ar da ta gabata ya nuna yadda sojoji ke ta harbi da bindigogi kan wasu mutane dake zaune jikin bango, fuskokinsu na kallon kasa.
Yayin wani taron manema labarai da ya gudana jiya a Yaounde babban birnin kasar, Issa Bakary ya ce gwamnati ta yi tir da wannan bidiyo da ta bayyana a matsayin na rashin imani da ba za a amince da shi ba. Ya kara da cewa, yayin da ake zargin sojojin kasar, daga cikin bidiyon akwai wata murya dake cewa sojojin wata kasa ne suka aikata kisan.
Jawabin nasa na zuwa ne bayan rahoton da wata kungiyar kasa da kasa ta fitar, ta na mai cewa sojojin Kamaru ne suka aikata kisan yayin wani aiki da suka yi a kauyen Achigaya dake yankin arewa mai nisa na kasar.
Ministan ya ce sojojin Kamaru masu da'a ne da suka san aikinsu, kana suna da kyakkyawar alaka da jama'a. Sai dai kuma ya sanar da cewa ana gudanar da bincike a kai.
Har ila yau, ya ce yanzu haka, akwai hukumar dake jagorantar bincike kan lamarin domin gano wadanda ke da hannu. Ya ce idan aka gano sojojin Kamaru ne, to za a gurfanar da su gaban kotu. (Fa'iza Mustapha)