in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta baiwa Kamaru tabbacin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali
2018-02-13 10:24:40 cri
A ranar Litinin Najeriya ta sake tabbatarwa jamhuriyar Kamaru cewa ba za ta taba laminta a yi amfani da yankunanta ba wajen ta da hankalin kasar Kamaru.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi wannan alkawari cikin wata sanarwar da aka fitar bayan kammala taron kwamitin tabbatar da tsaron iyakokin kasashen Najeriya da Kamaru karo na 6 wanda ya gudana a Abuja, hedkwatar mulkin Najeriyar.

Ya ce akwai matsalolin rikice-rikicen siyasa da suka dabaibaye kasashen biyu, lamarin da ya haifar da sabbin kalubalolin tsaro, inda hakan ke yin barazana ga zaman lafiya a tsakanin iyakokin kasashen biyu.

Birgediya janar Emmanuel Ndagi, daraktan al'amuran tsaro na ofishin babban mai baiwa shugaban kasa shawarar kan al'amuran tsaro, da ministan kula da yankuna na Jamhuriyar Kamaru Rene Sadi sun sa hannu kan wannan Sanarwar bayan taron.

Kasashen biyu sun amince da cewa, za su hada gwiwa wajen yakar almundahanar kudade da yaki da masu tallafawa ayyukan ta'addanci.

Ban da haka, kasashen biyu sun amince da yin hadin gwiwa wajen wayar da kan 'yan Najeriya dake zaune a yankin Bakassi don su kasance masu bin doka da oda kuma su zauna lafiya da al'umomin da suke rayuwa cikinsu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China