in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamaru: Za a gudanar da babban zabe lami lafiya a yanki mai amfani da Turanci Ingilishi
2018-08-21 10:54:56 cri
Minista mai kula da harkokin yankuna na kasar Kamaru Paul Atanga, ya ce za a gudanar da babban zabe a yankunan kudu maso yammaci da arewa maso yammacin kasar ta Kamaru, inda ake amfani da Turanci Ingilishi, a watan Oktoba mai zuwa, duk da damuwar tashin hankalin da ake samu a yankunan.

Ministan ya bayyana haka ne a ranar Litinin, ga taron manema labaru, bayan ziyarar gani da ido da ya kai wadannan yankuna, inda ya kara da cewa, bisa binciken da hukumomin kasar suka yi, akwai 'yan ta'adda a wasu 'yan wurare. Kana sojojin kasar na daukar matakai daban daban don tabbatar da kwanciyar hankali a wadannan yankuna 2.

Tun a watan Nuwamban bara, sojojin gwamnatin kasar suke arangama da dakarun 'yan aware, wadanda ke neman ballewar yankunan 2 daga kasar, tare da kafa kasar "Ambazonia".

MDD na cewa, ya zuwa yanzu fiye da mutane 160,000 ne suka raba da matsugunansu sakamakon tashin hankalin da ya abku a wadannan yankuna 2, kana kimanin wasu 30,000 kuma na gudun hijira a Najeriya

Kalaman ministan na zuwa ne bayan da dakaru 'yan aware suka yi barazanar yin zagon kasa a babban zaben da ake shirin gudanarwa. A cewar ministan, an dauki matakan da suka dace na ganin an maido da zaman hankali a yankunan kafin zaben. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China