Kakakin babban sakataren, Stephane Dujarric, shi ne ya sanar da wannan rahoto a jiya Talata, inda ya ce rahoton ya nuna ci gaban da aka samu a shekarar da ta gabata a kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kare hakkin dan Adam, gami da neman samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa a kasashe daban daban.
Haka zalika, rahoton ya jaddada muhimmancin hulda da membobin MDD, da kungiyoyi na wasu shiyyoyi, da na kasa da kasa, gami da wasu kungiyoyin al'umma, don neman samun bakin zaren warware matsalolin da ke adabar duniya, wadanda wata kasa ita kadai ba za ta iya daidaita su ba. (Bello Wang)