in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya yi maraba da shirin zabe a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo
2018-08-14 09:33:09 cri
Kwamitin tsaron MDD ya yi maraba da irin shirye-shiryen da ake yi, game da babban zaben da za a gudanar a watan Disamba a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo.

Cikin wata sanarwar da aka fitar, mambobin majalissar sun yaba da yadda aka kammala tattara sunayen 'yan takara a zaben dake tafe, da ma irin yadda shugaban kasar mai ci Joseph Kabila, ya tabbatar da kudurinsa na biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar, da ma martaba alkawarin gudanar da zabe da aka cimma tun a ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2016.

Bisa yarjejeniyar karshen shekarar 2016, shugaba Kabila, wanda ke rike da ragamar mulkin jamhuriyar dimokaradiyyar Congo tun daga shekarar 2001, bayan hallaka mahaifinsa tsohon shugaban kasar Laurent Kabila, ba shi da hurumin tsayawa takara a zaben kasar na karshen shekara.

A baya dai an amince da gudanar da babban zaben kasar a ranar 27 ga watan Nuwambar shekarar 2016, amma sai aka dage zaben zuwa shekarar 2017. A karshe dai an amince a gudanar da babban zaben a ranar 23 ga watan Disambar dake tafe.

Sanarwar kwamitin tsaron MDDr ta bayyana muhimmancin gudunmawar 'yan siyasa, da hukumomin kasar ta Congo, wajen ganin zaben ya gudana lami lafiya, ta yadda za a kai ga mika mulki cimin kyakkyawan yanayi. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China