in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin Afirka sun jinjinawa taron FOCAC
2018-01-26 10:08:57 cri
Ministocin harkokin wajen kasashen Tanzania, da Kenya da Najeriya sun jinjinawa ci gaban da aka samu karkashin dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka na FOCAC.

Da yake bayyana matsayar sa game da hakan, ministan harkokin wajen Tanzania Augustine Philip Mahiga, ya ce tun bayan taron FOCAC na birnin Johannesburg da ya gabata a shekarar 2015, an cimma nasarori da dama ciki hadda ganawar jami'an sassan biyu, da musayar ra'ayi da hadin gwiwar kasashe masu tasowa, wanda hakan ya karfafa kawance tare da bude kofar tunkarar kudurorin ci gaban karni, da bunkasar tattalin arzikin duniya cikin hadin gwiwa.

A na ta jawabin, ministar harkokin wajen kasar Kenya Amina Mohamed, ta ce Sin ta fidda tsare tsare 10 na hadin gwiwa tsakanin ta da kasashen Afirka yayin taron Johannesburg, wadanda za a aiwatar cikin shekaru 3, shirye shiryen da suka kunshi kudi har dalar Amurka biliyan 60.

Ta ce Sin na shirin karbar bakucin taron FOCAC na birnin Beijing nan gaba cikin wannan shekara, taron da zai kara fadada damammaki na tattaunawa game da batutuwan da suka shafi ci gaban nahiyar Afirka, da kara nazaratar hanyoyin hadin gwiwa tsakanin nahiyar da kasar Sin.

A daya bangaren kuma, jami'ar ta ce kawo yanzu kasar Sin ta sanya hannu kan yarjeniyoyi na hadin gwiwa kimanin 80 da kasashen Afirka daban daban, karkashin shawarar ziri daya da hanya daya. Kaza lika masu zuba jari na kasar Sin sun zuba jarin da ya kai dalar Amurka sama da biliyan 50, tare da samar da guraben ayyukan yi kusan 200,000 a kasashe daban daban na nahiyar karkashin wannan shawara.

A nasa bangaren kuwa, ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama cewa ya yi, dandalin FOCAC dama ce ta samar da managarcin hadin kai da Afirka ke martabawa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China