in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar IRGC ta Iran ta yi gargadi game da tattaunawa da Amurka
2018-08-02 14:04:25 cri
Jagoran rundunar sojojin juyin juya halin kasar Iran Manjo Janar Mohammad Ali Jafari, ya ce za su yi duk mai yiwuwa, don ganin Iran ba ta shiga wasu shawarwari da Amurka ba.

Gidan talabijin na Iran mai suna Press TV ya raiwato Mohammad Ali Jafari na cewa, al'ummar Iran ba za ta taba yarda a shiga tattaunawa da shaidanin shugaba ba, maimakon hakan za su dauki dukkanin matakai na ganin an kaucewa hakan.

A cikin makon jiya ne dai shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana yiwuwar bude wata kofa ta tattaunawa tsakanin sa da mahukuntan Iran game da batun yarjejeniyar nukiliyar kasar, gabanin kuratowar lokacin da Amurka ta alkawarta kakabawa Iran din sabbin takunkumin hana cinikayyar zinari da danyen mai.

Da yake maida martani game da hakan, ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif, ya ce kamata ya yi Amurka ta zargi kan ta, bisa ficewa da ta yi daga yarjejeniyar shekarar 2015 da aka cimma, game da nukiliyar kasar ta Iran.

Yayin wata ganawa da ministan harkokin wajen Iran a makon jiya, shugaban addinin kasar Ali Khamenei, ya ce Amurka na son maido da matsayin ta kan Iran, kwatankwacin wanda take da shi gabanin juyin juya halin kasar na shekarar 1979, kuma ba ta da bukatar rage burin ta.

Don haka Khamenei ya jaddada cewa, kasar sa ba za ta dogara da kalamai ko ma sanya hannun Amurka kan wasu yarjeniyoyi ba, kuma duk wata tattaunawa da tsagin Amurkan bata lokaci ce kawai.

Khamenei ya kara da cewa, za su ci gaba da zantawa da kasashen turai, domin kare hakkokin Iran, karkashin yarjejeniyar shekarar 2015 da aka cimma, duk da janyewar Amurkan daga yarjejeniyar a ranar 8 ga watan Mayun da ya gabata. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China