in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran zata iya jure takunkumin da Amurka ta aza mata
2018-07-30 09:49:51 cri
Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya ce kasarsa zata iya jure matsanancin yanayin da take ciki na fuskantar takunkumin da Amurka ta kakaba mata.

Tashar talabiji ta Press TV ta jiyo Zarif yana bayyana cewa, Washington ta jima tana amfani da takunkumi a bisa tarihin mu'amalarta da kasashen duniya, inda ta sha kakaba takunkumin ga kasashen duniya masu yawan gaske.

Yace dangane da barazanar Amurka na kakabawa Iran din takunkumi, yanayin Iran zai samu ingantuwa kasancewar dukkanin kasashen duniya suna goyon bayan Iran din kuma zasu yi amfani da wannan damar.

A cewarsa zasu juya za su yi amfani da wannan dama don sa kaimin samar da kayayyaki a kasar da ma fitar da kayayyakinta da ba su shafi mai ba zuwa ketare, kuma wannan ya nuna cewa dole ne Amurka ta sauya hanyar da take bi na batu aza takunkumi.

Takunkumin da Amurkar ta sanyawa Iran zai fara aiki a watan Ogusta da kuma Nuwamba, bayan da Amurkar ta janye daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a ranar 8 ga watan Mayu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China