Ministan watsa labaran kasar kana kakakin gwamnati Micheal Makuei shi ne sanar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua. Ya ce, bangarorin sun cimma daidaito kan galibin batutuwan da suke takaddama a kansu yayin zagaye na uku na tattaunawar zaman lafiyar kasar da aka fara ranar 13 ga watan Agusta a birnin Khartoum na kasar Sudan.
Ya ce, tattaunawar ta yanzu za ta mayar da hankali ne kan batutuwan da ba a warware ba, da yarjejeniyar raba madafun iko da ma matakan tsaro.
Sai dai kuma Makuei ya ce sun tattauna a kan batutuwan da suka shafi ikon mataimakan shugaban kasa, da kafa kwamitocin da za su tsara kundin tsarin mulki, da kwamitin shari'a da yawan jihohi da iyakokinsu. (Ibrahim)