An dai yayata sanarwar shugaba Salva Kiir ta kafar radio mallakar kasar a daren jiya Laraba. Rahotanni sun ce afuwar ta shafi dukkanin sassan 'yan adawar kasar da suka jima suna yakar dakarun gwamnati.
Matakin na zuwa ne bayan kusan shekaru 5, tsagin dakarun gwamnatin kasar na bata kashi da 'yan adawa, kafin a karshen makon jiya a kai ga cimma matsaya ta rarraba madafun iko, tsakanin sassan masu ruwa da tsaki a rikicin kasar.
An dai cimma matsayar rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo karshen rikicin ne a birnin Khartoum na kasar Sudan, a ranar Lahadin karshen makon jiya. (Saminu Hassan)