Cikin wata sanarwa da ta fitar a birnin Juba, JMEC ta yi maraba da sanya hannu kan yarjejeniyar da tsagin gwamnati da na 'yan adawar Sudan ta kudun suka yi, a birnin Khartoum, fadar mulkin kasar Sudan, tana mai kira da a tabbatar an aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.
Hukumar ta kuma yi maraba, da matsaya daya da aka cimma, game da wasu muhimman batutuwa da sassa masu adawa da juna a Sudan ta kudun ke takaddama a kan su. (Saminu Hassan)