in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta bukaci hadin kan kasa da kasa game da tallafawa shirin zaman lafiya a Sudan ta kudu
2018-08-14 09:49:07 cri
Ministan harkokin waje na kasar Sudan Al-Dirdiri Mohamed Ahmed, ya yi kira ga kasashen duniya da su marawa shirin wanzar da zaman lafiyar Sudan ta kudu baya.

Al-Dirdiri Mohamed Ahmed ya yi kiran ne cikin wata sanarwa da ya fitar, bayan ganawarsa da jakadun kasashen Amurka da Birtaniya, da Norway da hadaddiyar daular Larabawa a birnin Khartoum. Ministan ya ce yana fatan Amurka da Birtaniya da Norway, za su samar da taimako na kai tsaye ga Sudan ta kudu, domin cimma nasarar yarjejeniyar birnin Khartoum, wadda aka rattabawa hannu a ranar 5 ga watan Agustan nan.

Kaza lika ya bukaci a gaggauta gudanar da taron kasashen 3, tare da ministocin kungiyar raya gabashin Afirka ta IGAD, wadda ta shiga tsakani a batun cimma yarjejeniyar, taron da a cewarsa ya dace ya maida hankali ga lalubo hanyoyin samar da ci gaba a yankin.

A ranar 5 ga watan nan na Agusta ne dai sassan dake takaddama da juna a rikicin Sudan ta kudu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar wanzar da zaman lafiyar kasar a birnin Khartoum na Sudan, aka kuma raba madafun ikon kasar, tare da cimma matsaya game da batutuwan da suka jibanci tsaro. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China