in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka da Birtaniya da Norway sun ce yarjejeniyar zaman lafiyar Sudan ta Kudu ba za ta dore ba
2018-08-11 16:04:49 cri
Kasashen Amurka da Birtaniya da Norway, sun bayyana cewa, yarjejeniyar zaman lafiyar Sudan ta kudu da aka rattabawa hannu a baya-bayan nan a birnin Khartoum, a matsayin wadda ba za ta dore ba.

Wata sanarwar hadin gwiwa da kasashen uku suka fitar, ta ce akwai yiyuwar samun kalubale a nan gaba, kuma abun damuwar ita ce, yarjejeniyoyin da aka cimma ba masu yiyuwa ba ne, balle su dore.

Sanarwar ta kara da cewa, la'akari da gazarwarsu a baya, akwai bukatar shugabannin Sudan ta kudu su sauya takunsu, ta yadda za su nuna kudurinsu na son samar da zaman lafiya da kyakkyawan shugabanci.

Kasashen 3, sun jadadda cewa, suna sa ran ganin sauyin lamarin, ta hanyar fara wa da raguwar rikice-rikice, sannan dukkan bangarorin su dauki matakan bada damar kai agajin jin kai ga masu bukata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China