Kwamitin sulhun ya bayyana cewa tuni babban sakataren MDD Antonio Guterres ya amince da tsawaita aikin tawagar ta UNOCA zuwa karin shekaru uku nan gaba, wato daga ranar 1 ga watan Satumbar 2018 zuwa 31 ga watan Augastan shekarar 2021. Kwamitin sulhun ya bayyana aniyarsa na amincewa da wannan batu, kamar yadda sanarwar kwamitin sulhun MDDr ta bayyana.
Kwamitin sulhun MDDr ya bukaci Guterres da ya sake duba game da batun wa'adin aikin tawagar ta UNOCA ya kuma mika mata shawarwarin da ya zartar kafin ranar 1 ga watan Augastan shekarar 2019. (Ahmad Fagam)