in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan wasan kwallon tebur na Najeriya ya lashe gasar ITTF
2018-08-14 09:16:03 cri

Dan wasan kwallon tebur na Najeriya Aruna Quadri, ya lashe gasar hukumar ITTF, bayan da ya doke takwaransa na Faransa Hachard Antoine, a wasan karshe da ya gudana ranar Lahadi a jihar Lagos dake kudancin Najeriya.

Aruna Quadri ya samu nasarar daga kofin na shekarar 2018 ajin maza ne, bayan kwashe shekaru 5 yana hankoron cimma wannan nasara. Ya kuma samu nasara a wasan na karshe da ci 11-13, da 11-3, da 8-11, da 11-7, da kuma 11-5, 11-7.

Da yake tsokaci game da nasarar tasa, Quadri ya ce yanzu dai mafarkinsa ya tabbata, kasancewar tun shekarar 2013 yake shiga wannan gasa ba tare da cimma nasara ba. Ya ce nasarar tasa na da nasaba da irin kauna da goyon baya da yake samu daga masu goya masa baya. A cewarsa wannan ne karo na 2 da ya kai ga wasan karshe, kuma yana alfahari da ganin ya cimma burinsa na daga kofin gasar. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China