in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta inganta ci gaban abubuwan hawa masu amfani da sabbin makamashi yadda ya kamata
2018-01-22 13:09:01 cri
Kwanan baya, an shirya taron dandalin tattaunawa game da abubuwan hawa masu amfani da sabbin makamashi na kasar Sin na shekarar 2018. Ministan kula da harkokin kimiyya na kasar Sin Wan Gang ya bayyana cewa, a shekarar 2017, yawan abubuwan hawa masu amfani da sabbin makamashi da aka sayar a wasu muhimman kasashe ya wuce miliyan daya da dubu 420, ciki kuwa hadda wadanda yawansu ya kai kimanin dubu 777 a nan kasar Sin. Ya zuwa yanzu, an riga an cimma nasarar kammala tsarin samar da ababen hawa tun daga sarrafa sassan su zuwa hada su, kana an samu ci gaba wajen nazarin muhimman fasahohin harhada kayayyakin mota, kana an samu saurin bunkasuwar kasuwar su.

Baya ga haka, Wan Gang ya fayyace cewa, a nan gaba kasar Sin za ta bi hanyar amfani da makamashin lantarki kana ta zamani, da kara mai da hankali kan kirkire-kirkiren masana'antu, da fasahohi da kuma manufofi, da nufin ciyar da abubuwan hawa masu amfani da sabbin makamashi gaba yadda ya kamata.

An sanya "Nazarin yanayin yin kwaskwarimar duniya, da tabbatar da samun ci gaba yadda ya kamata" a matsayin babban taken taron dandalin tattaunawar na kwanaki biyu, wanda mahalartansa suka fito daga gwamnatoci, da sassan masana'antu, da jami'o'i da kuma kwalejojin nazarin kimiyya na kasar Sin da na kasashen ketare. Sassan sun tattauna tare kan samar da yanayi mai kyau ga bunkasa abubuwan hawa masu amfani da sabbin makamashi. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China