Tashar mai karfin kilovolt 800, za ta hade lardunan kasar 5 da ya kai kilomita 1,600, wanda ya fara daga yankin Qinghai mai tsaunuka dake arewa maso yammacin kasar, zuwa yankin Henan mai yawan jama'a dake tsakiyar kasar Sin, kamar yadda hukumar samar da lantarki kasar Sin shiyyar lardin Qinghai ta sanar. (Ahmad Fagam)