in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Makamashi mai tsafta ya kai kaso 75 bisa dari na yawan makamashin da aka samar a lardin Qinghai
2018-01-10 11:02:03 cri
Mahukuntan lardin Qinghai dake arewa maso yammacin kasar Sin sun bayyana cewa, adadin makamashi mai tsafta da lardin ya samar a bara ya kai kaso 75.2 bisa dari, na daukacin nau'in makamashin lardin.

Wasu bayanai daga hukumar dake lura da harkokin raya tattalin arziki da fasahar sadarwa ta lardin, sun tabbatar da cewa a shekarar ta 2017, cibiyoyin samar da makamashi sun samar da adadin da ya kai biliyan 61.6 bisa ma'aunin "kilowatt hour" na lantarki, adadin da ya karu da kaso 11.4 bisa dari bisa na shekarar da ta gabata.

Bayanan sun shaida cewa, adadin makamashin da aka samu daga cibiyoyin sarrafa kwal ya karu da kaso 1.45 bisa dari a shekara guda, inda ya kai kusan biliyan 15.3 bisa ma'aunin "kilowatt hour". Kaza lika makamashin da ake samar wa daga cibiyoyin ruwa, da na iska, da na hasken rana ya kai biliyan 46.3 bisa ma'aunin "kilowatt hour".

Bisa jimilla, sashen samar da makamashi ta ruwa na da kaso 9.9 bisa dari, sai na hasken rana mai kaso 25.9, yayin da na karfin iska ke da kaso 76.8 bisa dari.

Domin yaki da gurbatar muhalli, kasar Sin na gwada dabarun samar da makamashi ta hanyoyi mabambanta, tare da kaucewa dogaro kacokan kan kona kwal, da fadada amfani da dabarun samar da makamashi mai tsafta.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China