in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na fatan inganta hadin gwiwa da hukumar IEA
2017-12-09 12:46:14 cri
Mataimakin Firaministan kasar Sin Zhang Gaoli, ya ce kasarsa na fatan aiki da hukumar IEA mai kula da makamashi ta duniya, da nufin hada gwiwa a bangaren makamashi.

Zhang Gaoli ya bayyana haka ne a jiya, lokacin da yake ganawa da Daraktan zartarwa na hukumar IEA Fatih Birol a nan birnin Beijing.

Ya ce a matsayinta na kasa da ta fi samarwa tare da amfani da makamashi, kasar Sin na ba batun inganta sauya fasalin makamashi muhimmanci.

Ya ce kasar Sin za ta yi yunkurin cimma burin kirkire kirkire da samarwa da raya makamashi mara gurbata muhalli ga al'ummarta, da karfafa raya masana'antu dake amfani da makamashi mai tsafta da samar da sauyi a yanayin samarwa tare da amfani da makamashi da zai kasance mai tsafta da inganci, wanda ba shi da hadari da yawan sinadarin Carbon.

Har ila yau, ya ce kasar Sin na fatan aiki da hukumar wajen bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a wannan fanni, da ma samar da ci gaba a bangaren amfani da makamashi maras gurbata muhalli a Sin.

A nasa bangaren, Fatih Birol, ya ce kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen karfafa gwiwar amfani da makamashi mai tsafta da rage hayakin Carbon a duniya.

Ya ce hukumar na fatan karfafa hadin giwa a dukkan fannoni da kasar Sin, ta yadda za su hadda hannu wajen inganta raya makamashi da sake masa fasali a duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China