in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping zai jagoranci taron kolin FOCAC a Beijing
2018-08-20 15:43:55 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya sanar a yau Litinin cewa, za'a kira taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka ko kuma FOCAC a takaice a birnin Beijing a ranakun 3 zuwa 4 na watan Satumbar bana. Babban taken taron shi ne, yin hadin-gwiwa da samun moriya tare, da kara raya makomar al'ummar Sin da Afirka ta bai daya kafada da kafada.

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai jagoranci taron kolin gami da halartar wasu ayyuka. Wasu shugabanni na kasashe membobin FOCAC za su zo Beijing don halartar taron, haka kuma wakilai daga kungiyoyin Afirka da na kasa da kasa za su hallara.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China