in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da firaministan Mauritius
2018-07-29 15:28:05 cri

 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping a jiya Asabar ya bayyana cewa a koda yaushe kasar Sin a shirye take ta kasance kyakkyawar kawa kuma kyakkyawar aminiyar hadin gwiwa ga kasar Mauritius da kuma cigaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon matsayi.

Xi ya yi wannan tsokaci ne a lokacin ganawa da firaministan kasar Mauritius Pravind Jugnauth a lokacin da ya yada zango don yin ziyarar kyautata zumunta a kasar ta Mauritius.

Shugaban na Sin ya ce kasashen biyu za su kiyaye matsayin mu'amalarsu zuwa babban matsayi, da karfafa matsayin alakar dake tsakanin sassan gwamnatocin kasashen biyu, da kuma dangantakar dake tsakanin majalisun dokokin kasashen biyu, kuma za su cigaba da nuna fahimtar juna da tallafawa juna game da batutuwan da suka shafi moriyar kasashen biyu bisa manyan tsare tsare.

Ya kamata bangarorin biyu su sake duba yiwuwar kara hadin kai, da inganta matsayin huldar cinikayya da zuba jari a tsakaninsu, da kuma cimma matsaya game da yarjeniyoyin da kasashen biyu suka rattaba hannu kansu na yin cinikayya cikin 'yanci, da kawar da duk wani shinge domin kasar Mauritius ta samu damar shiga a dama da ita bisa shawarar "Ziri daya da Hanya daya", da karfafa musayar bayanai, da zurfafa hadin gwiwa bisa dukkan fannoni, in ji shugaba Xi.

Jugnauth ya sake gabatar da sakon fatan alheri zuwa ga shugaba Xi bisa yadda yake cigaba da kyautata dadaddiyar dangantakar abokantaka dake tsakanin Sin da Mauritius.

Ya ce kasar Mauritius ta yabawa kasar Sin bisa tallafi da kuma taimakon da take ba ta a dogon lokaci, kuma tana dora muhimmanci ga cigaban da kasar Sin ta samu a sabon zamani, tana farin ciki da muhimman nasarorin da kasar Sin ta cimma, kuma ya nuna yabo ga manufofin shugaba Xi game da gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama.

Mauritius za ta cigaba da rungumar manufofin kasar Sin, ta yi maraba da shawarar "Ziri daya da Hanya daya", kuma a shirye take ta zurfafa mu'amalar hadin gwiwa tare da kasar Sin, in ji Jugnauth.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China