in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya koma gida bayan kammala ziyara a Asiya, Afrika da kuma taron kolin BRICS
2018-07-29 20:14:39 cri

A yau Lahadi shugaban kasar Sin Xi Jinping ya koma birnin Beijing bayan kammala ziyarar aiki da ya kai hadaddiyar daular larabawa (UAE), da Senegal, da Rwanda da kuma Afrika ta kudu.

A lokacin ziyararsa a kasar Afrika ta kudu, shugaba Xi ya halarci taron kolin BRICS karo na 10 a Johannesburg. Haka zalika, shugaban na Sin ya yada zango don gabatar da ziyarar sada zumunta a kasar Mauritius a yayin da yake kan hanyarsa ta komawa Beijing.

A daidai lokacin da ya tashi daga Port Louis zuwa Beijing, Xi ya bayyana cewa, ziyarar sada zumunci ta Mauritius ta tabbatar da samun nasarar kammala ziyararsa a nahiyoyin Asiya da Afrika. Koda yake ziyarar ta kasar Mauritius gajeriya ce, amma kuma ta haifar da gamsasshen sakamako kuma mai muhimmanci, wanda tabbas zai taimaka wajen karfafa huldar dake tsakanin Sin da Mauritius, in ji shugaba Xi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China