in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya bukaci a kara kaimi wajen sadaukar da kai da nuna kishin kasa
2018-08-06 16:00:49 cri
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bukaci a kara himma wajen sa kaimi don nuna kishin kasa da sadaukar da kai kamar yadda wani jami'in sojin kasar Sin ya nuna bajinta inda ya shafe shekaru kimanin 32 yana gadin tsibirin island post na kasar.

Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin tsakiya na rundunar sojojin kasar Sin ya ce bisa la'akari da rayuwar Wang Jicai, wanda tsohon jami'in soji ne mai tsaron yankin tsibirin Kaishan dake lardin Jiangsu na gabashin kasar Sin, ya kasance abin koyi ga al'ummar sabon karni wajen sadaukar da kai da yin aiki tukuru da tsohon jami'in tsaron ya nuna. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China