in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya taya zababben shugaban kasar Zimbabwe murna
2018-08-07 14:29:11 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taya Emmerson Mnangagwa murnar lashe zaben shugaban kasar Zimbabwe.

A sakon taya murnar da ya aike masa a ranar Lahadi, Xi Jinping, ya bayyana fatan gwamnati da al'ummar Zimbabwe za su samu ci gaba karkashin shugabancin Emmerson Mnangagwa.

Shugaba Xi ya ce ya na sa ran kara ganawa da Shugaba Mnangagwa don musayar manufofi kan dangantakar kasar Sin da Zimbabwe, a lokacin da zai halarci taron koli na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Afrika da za a yi a watan Satumba a nan birnin Beijing.

Xi yana fatan ganawar da zai yi da Shugaban na Zimbabwe, ta bude kofar kulla dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, ta yadda dukkansu za su amfana. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China