Ita ma babbar jam'iyyar adawa ta 'yan gurguzu wato SPD da tsohon shugaban majalisar dokokin Tarayyar Turai Martin Schulz ke jagoranta ta samu gagarumin koma baya.
Sai dai ba zato, jam'iyyar AFD ta samu gagarumin ci gaba inda ta samu kaso 13.5 na kuri'un, al'amarin da ya sanya ta zama jam'iyya mai karfi ta uku a majalisar dokokin kasar.
A wani jawabin da ta yi bayan zaben da aka watsa ta talabijin, Merkel ta shaidawa magoya bayanta cewa, manufofin gwamnatinsu a bayyane suke, kuma babu wata gwamnati da za a kafa ba tare da su ba, ta na mai tabbatar da cewa jam'iyyarta ta cimma nasara a zaben duk da cewa ta yi fatan samun sakamakon da ya fi wannan. (Fa'iza Mustapha)