in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyun kasar Jamus suna tattauna yiwuwar kafa gwamnatin hadaka
2018-01-08 13:59:07 cri
Jam'iyyar kawancen CDU da CSU dake Jamus da jam'iyyar SPD ta kasar sun fara tattauna yiwuwar kafa sabuwar gwamnatin gamin-gambiza a jiya Lahadi.

Bangarori mahalarta taron na ganin cewa, tun da kasar Jamus ta riga ta shiga cikin wani sabon zamani, dole ana bukatar daukar sabbin manufofi da fasahohin gudanar da mulki don tinkarar kalubalolin da ake fuskantar a gida, gami da sauyin yanayi a duniya.

An gudanar da taron ne a hedkwatar jam'iyyar SPD dake birnin Berlin, fadar mulkin kasar ta Jamus. Bayan da aka kammala tattaunawa a jiya, an kuma sanar da cewa, baki daya za a shafe kwanaki 5 ana gudanar da shawarwarin na wannan karo, kana za a gabatar da sakamako da aka cimma a ranar Alhamis mai zuwa.

An ce a wajen shawarwarin da suka gudana jiya, an kasa jami'ai mahalarta taron zuwa rukunoni 15, wadanda suka tattauna batutuwa a fannoni daban daban, kana shawarwarin da ake yi a wasu rukunoni na tafiya yadda ake bukata. Sai dai kafin lokacin da aka kammala dukkanin shawarwarin, ba za a bayyanawa jama'a abubuwan da aka tattauna ba.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China