Madam Angela Merkel ta yabawa kasar Sin saboda babbar gudummawar da ta bayar a fannonin da suka shafi tinkarar matsalar sauyin yanayi, da gudanar da cinikayya cikin 'yanci da sauransu, haka kuma ta ce, Jamus na fatan yin hadin-gwiwa tare da kasar Argentina wadda za ta jagoranci kungiyar G20 a karo mai zuwa, ta yadda harkokin kungiyar za su ci gaba da bunkasa.
Karfafa hadin-gwiwa tare da kasashen Afirka, wani batu ne da Jamus ke kokarin gudanarwa. A cewar Merkel, ya kamata kasashen G20 su yi koyi da kasar Sin a fannin raya hulda da Afirka. Merkel ta kuma ce, kasar Sin ta samu dimbin nasarori a fannonin kawar da kangin talauci, da habaka tattalin arziki, tare kuma da inganta muhimman ababen more rayuwar al'umma.(Murtala Zhang)