in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta nuna damuwa game da halin da ake ciki a yammacin Afrika da Sahel
2018-08-11 15:54:59 cri
Kwamitin sulhun MDD ya sanar a ranar Juma'a cewa ya damu matuka game da yanayin kalubalolin tsaro da ake fama da shi a kasashen yammacin Afrika da yankin Sahel, kana ya bukaci hukumomin MDD dake yankunan da su hada kai don magance kalubalolin tsaron.

A wata sanarwar da shugaban kwamitin ya fitar, kwamitin sulhun ya bayyana matsalolin ta'addanci, fashin teku, da rikici tsakanin makiyaya da manoma da mugayen laifuka a tsakanin iyakokin kasashen da cewa sun kasance a matsayin manyan abubuwan dake barazana ga tsaro a shiyyoyin.

Kwamitin ya yi maraba da kokarin da ofishin MDDr na yammacin Afrika da Sahel (UNOWAS) ke yi wajen tallafawa aikin bincike game da halin da yankin ke ciki da kuma irin matakan gaggawa da ya kamata a dauka kan lamarin.

Game da batun aikata muggan laifukan a tsakanin kasashen kuwa, kwamitin MDD ya yi Allah wadai da ayyukan safarar bil adama, inda ya ce yana daya daga cikin abubuwan dake taimakawa wajen yaduwar wasu karin munanan laifuka kuma yana iya haddasa tashe tashen hankula, kana ya jaddada bukatar hukumar ta kara kokarinta karkashin tsarin MDD wajen shawo kan matsalar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China