Mataimakin kakakin Guterres Farhan Haq ya shaidawa taron manema labarai cewa, MDD ta ji sanarwar da gwamnatin Congon ta bayar cewa, Emmanuel Ramazani Shadary ne zai yiwa jami'iyyar dake mulki takara a zaben shugabancin kasar.
Ya ce, MDD ta kuma yi maraba da ci gaban da aka samu, wanda zai kai ga gudanar da zaben gaskiya da adalci a ranar 23 ga watan Disamban wannan shekara kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Shadary tsohon ministan harkokin cikin kasar DRC, shi ne babban sakataren jam'iyyar PPRD a halin yanzu.(Ibrahim)