in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: 'Yan fashi sun hallaka mutane 10 a jihar Edo
2018-08-10 19:22:52 cri
A kalla mutane 10 ne suka rasa rayuwar su, ciki hadda 'yan sanda 4 dake gadin wasu bankuna 2 dake garin Igarra a karamar hukumar Akoko Edo ta jihar Edo dake kudancin Najeriya.

Rahotanni daga jihar sun ce wasu 'yan fashi da makami ne suka afkawa bankunan dake Igarra a ranar Alhamis, kafin hakan kuma sai da suka kai farmaki wani ofishin 'yan sanda dake garin, lamarin da ya yi matukar tada hankulan mazaunan sa. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China