in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun fille kan wasu mutane 7
2018-08-07 19:26:03 cri
A Najeriya wasu mahara da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne, sun fille kan wasu mutane dake zaune a kauyen Munduri a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Rahotanni daga kauyen da wannan lamari ya faru sun nuna cewa, mayakan sun aukawa kauyen ne da almurun jiya Litinin, inda bayan hallaka wasu mazauna wurin, suka kuma cinnawa wasu gidaje da dama wuta, lamarin da ya yi matukar tada hankulan mazauna kauyen, kamar dai yadda Baba Ali Daudu, wani mazaunin kauyen na Munduri ya bayyana. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China