in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 9 sun nitse a kogin arewa maso gabashin Najeriya yayin da suke shakatawa
2018-08-06 10:55:12 cri

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da cewa matasa 9 ne suka nitse a lokacin da suke shakatawa a gefen kogin jihar Taraba a arewa maso gabashin kasar.

Masu aikin ceto sun tsamo gawawwakin mutane 7 tun lokacin da abin ya faru a ranar Asabar, in ji Hukumar kula da matasa masu bauta wa kasa wato (NYSC).

Dukkan wadanda suka mutu mambobi ne na hukumar NYSC, wadda gwamnatin Najeriya ce ta kafa ita.

Florence Yaakugh, shi ne wani jami'i na hukumar NYSC na jihar, ya shedawa manema labarai cewa matasan 22 ne suka tafi bakin kogin Mayo-Selbe dake yankin Gashaka na jihar Taraba domin shakatawa inda daga bisani lamarin ya auku.

Yaakugh ya ce, har yanzu masu aikin ceto suna ci gaba da kokarin gano ragowar gawawwakin mutane biyu, inda ya bayyana lamarin da cewa abin bakin ciki ne matuka.

Sai dai sakamakon binciken farko da jami'an 'yan sanda suka gudanar ya nuna cewa, matasan suna ninkaya ne a cikin kogin, inda daga bisani ruwan kogin ya tumbatsa ya yi awon gaba da su.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China