in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya yi maraba da rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin bangarorin Sudan ta kudu
2018-08-07 09:40:00 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi maraba da yarjejeniyar shawo kan takkadamar shugabanci da raba iko tsakanin bangarori masu adawa da juna a Sudan ta Kudu da aka rattabawa ranar Lahadi a birnin Khartoum na Jamhuriyar Sudan.

Antonio Guterres, ya ce rattaba hannu kan yarjejeniyar muhimmin mataki ne na farfado da yarjejeniyar warware rikici a Sudan ta Kudu da aka rattabawa hannu a ranar 17 ga watan Augustan 2017 a birnin Addis Ababa na Habasha.

Sakatare Janar din ya kuma yabawa shugabancin kungiyar raya yankin gabashin Afrika IGAD da ya jagoranci taron sulhun, da kuma kokarin Jamhuriyar Sudan na samar da yarjejeniyar warware matsalolin siyasa na rikicin Sudan ta Kudu.

Da yake waiwaye game da yarjeniyoyin da bangarorin biyu suka cimma a baya, Antonio Guterres ya bukaci dukkan bangarorin, su yi aiki da zuciya daya, don nuna kudurinsu na aiwatarwa da kammala farfado da yarjejeniyar warware rikicin kasar nan bada dadewa ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China