Ya ce, MDD za ta hada kai da wadanda makamin kare dangin ya yiwa illa domin ganin an kawar da makaman nukiliyar kwata-kwata a duniya.
A ranar Talata ne Guterres ya isa kasar Japan, a ziyarasa ta biyu zuwa kasar tun bayan da ya hau kan wannan mukami. Ya kuma gana da firaminista Shinzo Abe na Japan jiya da safe.
A ranar 6 da kuma 9 ga watan Agustan shekarar 1945 ne sojojin Amurka suka jefa makamin kare dangi a biranen Hiroshima da Nagasaki na kasar Japan, don tilastawa Japan ta yi saranda a yakin duniya na biyu. A ranar 15 ga watan Agustan shekarar 1945, kasar ta Japan ta mika wuya ga sojojin kawance, abin da ya kawo karshen yakin.(Ibrahim)