Yayin wani taron manema labarai a hedkwatar MDD dake birnin New York, Zeid Al Hussein, ya ce wadanda aka bautar ta hanyar lalata a Koriya ta kudu da Koriya ta arewa da kasar Sin da sauran kasashe, na kara girma, kuma suna da bukatar sanin ko za a yi raradin da suke ji adalci.
Jami'in wanda ya ce ya kamata a gaggauta daukar mataki, ya ce wannan shi ne kiran da zai yi ga gwamnatin Japan.
Ya kuma bayyana fatan Japan za ta yi komai a bayyane game da yuwuwar sake gyara ka'idojin yarjejeniyar da aka cimma da Koriya ta arewa a shekarar 2015 kan batun, wadda wadanda lamarin ya shafa da gwamnati mai ci suka ki amincewa da ita. (Fa'iza Msutapha)