in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An damke wani kwamandan Boko Haram a Najeriya
2018-08-05 20:45:58 cri
Rundunar sojan kasa ta Najeriya ta tabbatar da damke wani kwamandan kungiyar Boko Haram da ake nema ruwa a jallo.

Mai magana da yawun rundunar Texas Chukwu wanda ya tabbatar da hakan a yau Lahadi, ya ce, wanda ake zargin mai suna Maje Lawan, shi ne na 96 cikin jerin sunayen 'yan ta'addan da rundunar sojan ta dade da wallafawa.

Texas Chukwu ya ce, sojojin sun yi nasara damke wanda ake zargi ne a garin Banki dake makawbtaka da jihar Borno a yankin arewa maso gabashin kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China