An ratsa da akwatin gawar Simegnew Bekele ta titunan birnin Addis Ababa, inda kuma aka binne shi a babbar mujami'ar Cathedral ta kasar.
An samu gawar Injiniyan cikin motarsa da raunin harbi a ka, a ranar Alhamis da ta gabata.
Gomman masu makoki ciki har da shugaban kasar Mulatu Tshome ne suka yi ban kwana da marigayin.
Bekele, ya kasance babban Injiniyan dake jagorantar babbar madatsar ruwan Habasha mai karfin mega watt 6,450 tun da aka fara aikin a watan Afrilun shekarar 2011 a cikin Kogin Blue Nile.
Idan aka kammala aikin wanda a yanzu ke kan kashi 66 bisa 100 na kammaluwa, zai zama irinsa mafi girma a nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)