Shugaba Afwerki ya ziyarci rukunin masana'antun ne bayan halartar wata gagarumar liyafar maraba da firaminista Abiy Ahmed da shugaban kasar Habashan Mulatu Teshome suka shirya masa a fadar shugaban kasar.
A cewar shugaban ma'aikata a ofishin firaministan Habasha Fitsum Arega, firaminista Ahmed ya bayyana rukunin masana'antu na Hawassa a matsayin wata alama ta ci gaban masana'antun kasar, kuma ya kasance abin koyi ga ragowar rukunonin masana'antun dake sassan kasar, duba da irin nasaraorin da ya cimma tun lokacin da aka kaddamar da shi a watan Yulin shekarar 2016, ta hanyar janyo hankulan manyan kamfanonin saka tufafi na duniya cikin kasar.
A baya gwamnatin kasar Habasha ta bayyana cewa, da zarar ya fara aiki rukunin masana'antun zai samar da kudaden shigar da suka tassama dala biliyan 1 a duk shekara.
Rahotanni na nuna cewa, a duk lokacin da shugabannin Afirka suka ziyarci kasar Habasha, su kan je rukunin masana'antun, shugaba na baya-bayan da ya ziyarci rukunin masana'antun na Hawassa, shi ne shugaba Paul Kagame na Rwanda,wanda ya kai ziyara a watan Mayun wannan shekara. (Ibrahim Yaya)