in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tanzania da China sun gamsu da hadin gwiwarsu kan adana namun daji
2018-02-07 09:33:09 cri
Mahukuntan kasashen Tanzaniya da Sin da jami'an diplomasiyya sun yaba da hadin gwiwar kasashen biyu a fannin kula da gandun daji.

Haka zalika kasashen biyu sun yi alkawarin karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu ne a lokacin da suka halarci taron koli na Sin da Tanzaniya kan al'amurran gandun daji da bunkasa fannin yawon bude ido, wanda ya gudana a Dar es Salaam, birnin kasuwancin kasar.

Gaudence Milanzi, babban sakatare a ma'aikatar kula da albarkatun kasa da yawon bude ido na kasar Tanzaniya, ya ce kasar Tanzaniya tana daukar kasar Sin a matsayin muhimmiyar abokiyar hulda a fannin kula da gandun daji.

Milanzi ya ce, abu ne a bayyane karara cewa, makomar fannin gandun daji ya dogara ne kan shigowar bangarori daban-daban wajen tsarawa da kuma aiwatar da dukkan matakan da suka dace na yaki da masu farautar namun dawa.

Hu Zhengyue, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin diplomasiyya na kasar Sin, wanda suka gudanar da taron kolin na hadin gwiwa da hukumar kula da yawon shakatawa ta Tanzaniya, da ofishin jakadancin Sin a Tanzania, ya ce kasar Sin ta himmatu matuka wajen kare rayuwar namun daji.

Ya ce matakin da kasar Sin ta dauka na haramta cinikin hauren giwa a dukkan kasuwannin kasarta, alamu ne dake nuna cewa kasar ta damu matuka game da batun kare namun daji.

Xu Chen, jami'in ofishin diplomasiyyar Sin a Tanzania, ya ce gwamnatin kasar Sin tana hada gwiwa da al'ummar kasa da kasa wajen kare al'amurran gandun daji. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China