Gasar wanda mutane 25 suka fatata a zagayen karshe, an kammalata a daren Jumma'a a birnin Dar es Salaam na kasar Tanzaniyar.
An shafe watanni da dama ana fafatawa tsakanin 'yan takarar da suka fito daga yankin Zanzibar da kuma yankunan Mwanza da Dar es Salaam na kasar Tanzania, inda aka gudanar da gasar.
Wannan shi ne karo na biyu da kamfanin Star Times ya gudanar da wannan gasa wanda ya hada da tashar watsa shirye shirye ta Star Swahili. A bara ma, kimanin 'yan Tanzaniyan 10 ne suka samu nasarar lashe wannan gasa, inda a halin yanzu sun zama ma'aikatan kamfanin wanda hedkwatarsa ke birnin Beijing, na kasar Sin
A shekarar da ta gabata rukunin kamfanin ya gudanar da gasar daukar murya na wasan kwaikwayo a Tanzania inda kuma masu shawa'ar shiga gasar suka samu guraben aikin yi a kasar Sin. (Ahmad Fagam)