Babbar sakatariyar ma'aikatar Dorathy Mwanyika ta ce kasar da bankin duniya, sun dauki hayar kamfanin IGN na Faransa domin samar da tsarin kula da filaye da ya kunshi dukkan bangarori, wanda zai mayar da duk batutuwan da suka shafi filaye kan na'urar kumfyuta.
Dorathy Mwanyika ta ce ta wannan hanya, suna fatan inganta aikin bada shaidar mallakar filaye tare da kara samarwa gwamnatin kudin shiga.
Ta ce a shekarar kudi ta badi ne za a fara amfani da wannan tsari a birnin Dar es Salaam, inda ta ce idan ya yi nasara, za a fadada shi zuwa fadin kasar.
Babbar sakatariyar ta ce ma'aikatar ta kuduri niyyar tabbatar da kyautata tsarin hayar filaye a kasar, ta yadda ba za a samu wata kafa ta yin magudi daga bangaren ma'aikata marasa gaskiya ba. (Fa'iza Mustapha)