in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta lashi takobin karfafa hadin gwiwa da Tanzania
2017-11-10 12:58:28 cri

Jakadar kasar Sin da ke kasar Tanzania Wang Ke, ta ce kasar Sin za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwa da Tanzania tare da ba da gudunmmuwa ga kasar dake gabashin Afrika, a kokarin da take na raya harkokin masana'antu.

Wang Ke, ta ce hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Tanzania zai kara karfi da fadada, wanda kuma zai kawo karin damarmaki ga huldar dake tsakaninsu da kuma ci gaban Tanzania.

Yayin wani taron manema labarai a birnin Dar es Salaam, Jakadar ta ce, ta yi imanin cewa, nan gaba karkashin jagorancin Shugaba John Magufuli da kokarin al'ummar kasar, burin kasar na habaka bangaren masana'antu tare da zama kasa mai samun matsakaicin kudin shiga zai cika.

Ta kara da cewa, Tanzania tana more damarmaki da suka hada da albarkatu daga Allah da yanayin kasa da albarkar jama'a da kuma dadaddiyar kawance tsakaninta da kasar Sin.

Har ila yau, Wang Ke ta ce, Tanzania na kan hanyar "Ziri daya da hanya daya" a nahiyar Afrika, kuma tana daya daga cikin kasashen Afrika na farko-farko da suka kulla kawance da kasar Sin.

A cewarta, a matsayinta na sabuwar jakada, ba za ta yi kasa a gwiwa wajen cimma burin aikinta ba, kuma za ta yi kokari wajen ganin dangantakar ta haifar da dimbin sakamako. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China