Antonio Guterres, ya kuma yi maraba da sabon kudurin mambobin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS da takwararta ta kasashen yankin tsakiyar Afrika, na karfafa hadin kai a kan kalubaken tsaro da zaman lafiya.
Sanarwar da kakakinsa Farhan Haq ya fitar, ta ruwaito cewa, Guterres ya yi na'am, musammam da matakin da aka dauka ranar Litinin yayin taron da ya gudana a Lomen kasar Togo, na rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa kan yaki da manyan laifuffuka ya zuwa karshen 2018, da kuma kafa kwamitin ministoci da zai kula da aiwatar da matakan da aka dauka yayin taron. (Fa'iza Mustapha)