in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sudan ya jaddada goyon bayansa na tabbatar da zaman lafiya a Sudan ta kudu
2018-08-06 12:07:41 cri

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya jaddada aniyar kasarsa ta cigaba da goyon bayan matakan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a makwabciyar kasar Sudan ta kudu ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla tsakanin bangarorin dake adawa da juna a kasar.

A ranar Lahadi ne bangarorin dake yaki da juna a Sudan ta kudun suka sanya hannu kan yarjejeniayr karshe a Khartoum babban birnin kasar Sudan game da batun raba madafun iko da kuma wanzar da zaman lafiya da tsaro.

Shugaban ya tabbatar da cewa wannan yarjejeniya ta wuce batun rubutu a takarda kadai, yana mai cewa, gabanin a sanya hannu kan takardun, an riga an kuduri batun a cikin zuciya kana ya kasance a matsayin alkawari.

A nasa bangaren, shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir Mayardit ya yi alkawarin aiwatar da yarjejeniyar har a cikin zuciyarsa.

Da yake jawabi a lokacin bikin, madugun 'yan adawar Sudan ta kudu Riek Machar ya ce zaman lafiya shi ne kadai zabin da ya rage, ya kara da cewa, wadanda suka halarci bikin a wannan karo sun kasance a matsayin masu shiga tsakani wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma.

A ranar 25 ga watan Yuli, bangarorin dake fada da juna a Sudan ta kudu sun amince da yarjejeniyar raba madafun ikon, inda shugaban zai cigaba da rike matsayinsa a gwamnatin rikon kwarya, kana Machar zai kasance a matsayin mataimakin shugaban kasa na farko cikin mataimakan shugaban kasar 4 daga jam'iyyun siyasar kasar daban daban.

Karkashin yarjejeniyar, majalisar zartarwar gwamnatin rikon kwaryar za ta kunshi ministoci 35, da suka hada da ministoci 20 daga bangaren gwamnati, ministoci 9 daga bangaren da Machar ke jagoranta na 'yan tawayen SPLM-IO.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China