in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hu Chunhua ya gana da shugaba da firaministan kasar Burkina Faso
2018-07-13 14:43:53 cri
Mr. Hu Chunhua, mataimakin firaministan kasar Sin wanda ke ziyarar aiki a kasar Burkina Faso, ya gana da shugaban kasar Christian Kaboré, a Ouagadougou, fadar mulkin kasar.

Hu Chunhua ya mikawa shugaba Christian Kaboré sakon gaisuwa da na gayyata zuwa taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka FOCAC, da shugaba Xi Jinping ya aike masa. Mr Hu ya bayyana cewa, shugaba Xi yana ba huldar dake tsakanin kasashen Sin da Burkina Faso muhimmanci, kana ya tura shi ziyartar Burkina Faso ne musamman domin kara fahimtar juna da sada zumunta tsakanin kasashen biyu, ta yadda za a iya karfafa hadin gwiwa tsakaninsu daga dukkan fannoni. Har ila yau, ya ce bangaren Sin ya yaba da kudurin gwamnatin Burkina Faso na farfado da huldar diflomasiyya tsakaninta da kasar Sin, yana mai cewa Sin na son hada kai da Burkina Faso don kara fahimtar juna a fannin siyasa, da kara hadin gwiwa mai karfi domin bunkasa huldar dake tsakaninsu yadda ya kamata cikin hali mai dorewa.

A nasa bangaren, shugaba Christian Kaboré, ya nemi Hu Chunhua da ya mika gaisuwarsa da jinjina ga shugaba Xi Jinping. Ya kuma bayyana cewa, farfadowar huldar diflomasiyya tsakanin kasashen Burkina Faso da Sin ya bude wata hanyar samun makoma mai haske. Kuma Bangaren Burkina Faso na fatan za a kulla huldar hadin gwiwa irin ta 'yan uwataka tsakaninsa da Sin.

A lokacin da yake ganawa da firaminista Paul Kaba Thieba na kasar Burkina Faso, Mr. Hu ya kuma mika shi gaisuwar da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi masa.

Bayan ganawarsu, Mr. Hu Chunhua da Mr. Paul Kaba THIEBA sun halarci bikin bude ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Burkina Faso. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China