in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangaren Sin ya gamsu da yadda kasashen Rasha da Amurka suke kyautata huldarsu
2018-07-17 20:20:55 cri
Madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, bangaren Sin ya gamsu da ganin yadda kasashen Rasha da Amurka suke kyautata huldar dake tsakaninsu.

Madam Hua ta furta haka ne a wani taron manema labaru da aka shirya yau Talata a nan Beijing a lokacin da take ba da amsa game da ganawar da shugabannin kasashen Rasha da Amurka suka yi.

Madam Hua ta kara da cewa, kasashen Rasha da Amurka dukkansu muhimman mambobi ne na kwamitin sulhu na MDD, kuma su manyan kasashe ne wadanda suke da tasiri sosai a duniya, kana suna da muhimmin nauyi na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya. Bangaren Sin na farin ciki sosai da kokarin kasashen na kyautata dangantakar dake tsakaninsu.

Sin na fatan bangarorin Rasha da Amurka za su kara yin mu'amala da tattaunawa da kuma habaka hadin gwiwa a tsakaninsu. Madam Hua ta kuma nuna cewa, ganawar da shugabannin Rasha da Amurka suka yi a birnin Helsinki na kasar Finland ba za ta kawo illa ko kadan ga dangantaka dake tsakanin kasashen Sin da Rasha, ko tsakanin kasashen Sin da Amurka ba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China