in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Minisatan harkokin wajen kasar Sin ya gana da ministocin wajen kasashen Larabawa
2018-07-12 10:48:29 cri
Mamban majalisar koli ta gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya tattauna da ministocin kasashen wajen Palesdinu, Somaliya, Mauritania, Tunisiya, Yemen da na kasar Libya daya bayan daya.

A tattaunawarsa da ministan harkokin wajen Somaliya Ahmed Isse Awad, Wang ya ce, a ko da yaushe kasar Sin za ta taimakawa kasar Somaliya a kokarinta na tabbatar da tsaron ikon kasarta, da tsaron iyakokinta, kuma za ta tallafawa gwamnatin Somaliya wajen ciyar da sha'anin siyasarta gaba, da warware matsalolin zamantakewarta da kuma inganta aniyar tsarin shugabancin kasar.

A tattaunawarsa da Ismail Ould Cheikh Ahmed, ministan harkokin wajen kasar Mauritania, Wang Yi ya ce, kasar Sin a shirye take ta karfafa shawarar "ziri daya da hanya daya" da nufin daga matsayin huldar dangantakar dake tsakanin Sin da Mauritania gaba.

A zantawarsa da takwaransa na kasar Tunisiya Khemaies Jhinaoui, Wang ya bukaci dukkan bangarorin da su aiwatar da sakamakon da aka samu na taron hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa wato CASCF, kana su shiryawa taron kolin FOCAC wanda za'a gudanar a Beijing a watan Satumba.

Dukkannin ministocin kasashen wajen sun hallara ne don halartar taron ministocin CASCF karo na 8 wanda aka gudanar a ranar Talata a Beijing. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China