in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hua Chunying ta ce kasar Sin na bin dokokin WTO sosai
2018-07-17 20:13:12 cri
A kwanan nan, bangaren Amurka ya zargi kasar Sin cewa wai ba ta martaba dokoki da ka'idodin hukumar cinikayya ta duniya WTO. Game da wannan magana, a yayin taron manema labaru da aka shirya yau Talata a nan Beijing, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta mayar da martani, inda ta ce, mai basira shi ne wanda ya fahimci sauran mutane, kana mai hankali shi ne wanda ya san ciwon kansa.

A kwanakin nan, kasar Amurka ta fitar da wasu rahotanni, inda ta sha zargin kasar Sin, wai kasar Sin ba ta martaba dokoki da ka'idodin WTO, har ma ta yi amfani da wannan zargi a matsayin muhimmin dalilin da ya sa ta dauki matakan cinikayya na matsa wa kasar Sin lamba bisa radin kanta. Kan wannan batu madam Hua Chunying ta nuna cewa, "Idan har kasar Sin ba ta martaba dokoki da ka'idodin WTO, me ya sa ta nemi izinin zama mamban kungiyar? Dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin ta wancan lokaci ta yanke kudurin shiga cikin kungiyar shi ne ta amince cewa, mataki ne da ka'idodin da duk duniya suke martabawa domin bunkasuwar tattalin arzikin duniya na bai daya, ingiza yin cinikayya ba tare da shinge ba zai taimaka ga cimma burin samun moriya da nasara tare. A cikin shekaru 17 bayan da kasa Sin ta shiga cikin kungiyar, kasar Sin ba ta son canja niyyarta da ta yi, har ma tana gudanar da harkoki bisa alkawuran da ta dauka. Idan kasar Sin ba ta martaba dokoki da ka'idodin WTO ba, don me ta cika dukkan alkawuran da ta dauka a lokacin shigar ta cikin kungiyar? A cikin takardar 'Kasar Sin da WTO' da ta fitar kwanan baya, ta yi amfani da alkaluma da shaidu na zahiri domin bayyana yadda ta cika alkawuran da ta dauka daga dukkan fannoni. Idan kasar Sin ba ta martaba dokoki da ka'idodin WTO ba, don me ta nace wajen kare ruhu da muhimman ka'idodin WTO? Bangaren Sin ya amince da cewa, muddin aka martaba da kuma kare ka'idodin kasa da kasa bisa yarjejeniyar da aka kulla, za a iya kare martaba da fa'idar tsarin yin cinikayya tsakanin bangarori daban daban. A da ko yanzu, har ma a nan gaba, kasar Sin ba za ta dauki matakan radin kai bisa moriyarta kawai ba, ko ta karya muhimman ka'idodin kungiyar WTO kamar su 'bude kofa da yin cinikayya cikin 'yanci, da kasa nuna bambanci, kasa samar da sharudan musamman ko masu nuna bambanci'. A bisa muhimman ka'idodi, kasar Sin na tsayawa tsayin daka wajen bin dokoki, da cika alkaruwa da kuma sauke nauyin da aka dora mata."

Sannan madam Hua Chunying ta nuna cewa, gamayyar kasa da kasa na amincewa da kokarin kasar Sin wajen martaba dokoki da ka'idodin WTO, da cika alkawuran da ta dauka wa WTO. Mr. Robert Azevedo ya bayyana cewa, bayan da kasar Sin ta zama mamban kungiyar WTO a shekarar 2001, rawar da take takawa a kungiyar tana ta karuwa a kai a kai. Wannan abin alfahari ne, da ya isa a yaba mata. A hakika dai, kawo yanzu kasar Amurka ta riga ta fitar da rahotanni 16 game da yadda kasar Sin take cika alkawuran da ta dauka wa WTO, ban da rahoton da ta fitar a bana, a cikin sauran rahotanni 15, ba ta taba cewa wai kasar Sin "ta yi kuskure" ba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China