in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sweden: Firaiministan Habasha ya cancanci zama babban mai jawabi a taron MDD
2018-08-01 11:18:19 cri
Firaiministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya cancanci a ba shi matsayin babban mai jawabi a babban taron MDD da za'a gudanar a watan Satumba, in ji jakadan kasar Sweden a MDD Olof Skoog, wanda kasarsa ce ke kammala shugabancin taron kwamitin sulhun MDD.

Skoog ya ce, "Idan akwai wani jajurtacce, kuma shugaban da ya kafa tarihi a kasar Habasha wajen sauya al'amurra don tabbatar da zaman lafiya, shin bai dace a amince da ba shi matsayin babban mai jawabi a taron MDDr ba?".

Jakadan ya danganta sabon firaiministan na Habasha da kokarin tabbatar da samun zaman lafiya tsakanin kasar da makwabciyarta Eritrea.

Gwamnatin kasar Habasha karkashin shugabancin Abiy, ba zato ba tsammani ta sanar a ranar 5 ga watan Yuni cewa ta amince da sharrudan yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya ta shekarar 2000 tsakaninta da Eritrea. Habasha ta kuma sanar da cewa ta amince da sakamakon da MDD ta goyi bayansa na mikawa kasar Eritrea yankunan da ake takaddama kansu.

Haka zalika Abiy ya yi tattaki zuwa Eritrea kana ya sanya hannu kan cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya da kyautata alaka tare da shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki a ranar 9 ga watan Yuli, inda hakan ya tabbatar da kawo karshen yakin da ake da kasar da kuma tabbatar da wanzuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Ya lura cewa tashin hankalin da ya barke tsakanin Habasha da Eritrea ya kasance wani babban al'amari wanda ya dau hankalin al'ummomin kasa da kasa inda aka shafe kusan shekaru 20 ana ta kokarin lalibo bakin zaren warware matsalar. Nasarar da Abiy ya samu za ta iya zama abin koyi ga sauran shugabannin duniya, in ji shi.

Skoog ya sanar a ranar Litinin cewa, ya kamata kwamitin sulhun MDD ya duba yiwuwar dagewa Eritrea takunkumin da aka aza mata. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China